Connect with us

News

Sam Ba Ni Da Labari Kan Abin Da Ya Faru A Unguwar Rimin Zakara — Gwamnan Kano 

Published

on

1738884977005

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabiru Yusuf, ya ce; ba shi da masaniya kan abin da ya faru a Unguwar Rimin Zakara da ke Karamar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane uku da jikkata mutane da dama a yankin a sakamakon rusau da aka gudanar a yankin.

Advertisement

Gwamnan ya ce, “Sai shekaran-jiya cikin dare na samu labarin abin da ya faru. Ashe tsohuwar rigima ce ta kusan shekaru 30, tsakanin Jama’ar Rimin Zakara da Jami’ar Bayero”

SWAN Ta Karrama Ahmad Hamisu Gwale A Matsayin Gwarzon Mai Gabatar Da Shirin Wasanni A Kano

Gwamna Abba ya ce; nan take ya dauki matakin dakile fitinar tare da daukar matakan dakatar da ita cikin gaggawa.

Advertisement

Gwamnan ya bayyana haka a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin na Rimin Zakara a yammacin ranar Alhamis 06, ga watan Febarairun 2025.

A yayin ziyarar l, gwamnan ya yi alkawarin gina wa jama’ar yankin na Rimin Zakara katafaren Masallacin Juma’a a matsayin sadaka jariya ga wadanda suka rasu a dambarwar filayan yankin da Jami’ar Bayero.

Advertisement

Gwamnan ya yi kuma alkawarin samar da Asibitin sha-ka-tafi da samar musu da hanya da kai hasken wutar lantarki da rijiyoyin burtsatsai da bai wa iyalan mamatan jari da daukar dawainiyar karatun yaransu gwargwadon iko da kuma daukar nauyin jinyar wadanda suka ji rauni a yankin a yayin rusau da aka yi a makon da ya gabata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending