Labarai
Al’ummar Rimin Zakara Sun Gudanar Da Alqunut Domin Neman Diyyar Gonaki Da Gidajensu

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Al’ummar garin Rimin Zakara dake jihar Kano, maza da mata, sun fito kan tituna da hanyoyi domin bayyana damuwarsu kan rashin biyan su diyyar gonaki da gidajensu, sakamakon aikin titin jirgin kasa da gwamnatin tarayya ta ayyana.
Tun sama da shekara guda da gwamnati ta sanar da fara wannan aiki tare da alkawarin biyan diyyar, amma har yanzu ba a biya su ba, duk da kokarin da suka yi na neman hakkinsu.
NDLEA Ta Kama Dattijo Mai Shekaru 75 da Zargin Siyar da Kayan Maye ga Matasa
Malam Hassan Hamza Rimin Zakara, jagoran wannan al’umma, ya bayyana cewa sun dade suna kira ga gwamnati kan wannan lamari, amma babu wani ci gaba. Ya ce, tun da ba a biya su hakkin su ba, ba su da wani zabi illa su ci gaba da gudanar da nomansu a kan wadannan filaye.
Hakazalika, mai unguwar Rimin Zakara, Alhaji Yakubu Shehe, ya nuna damuwar al’ummarsa kan halin da suke ciki, inda ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da su kawo musu daukin gaggawa.
Ya kuma yi kira ga Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya sanya baki domin ganin an biya al’ummar yankin hakkinsu.
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
