Sports
SWAN Ta Karrama Ahmad Hamisu Gwale A Matsayin Gwarzon Mai Gabatar Da Shirin Wasanni A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar Ƴan jaridu marubuta labaran wasanni ta ƙasa reshen jihar Kano ta karrama Ahmad Hamisu Gwale na Premier Radio Kano a matsayin gwarzon mai gabatar da labarin wasanni na shekarar 2024.
Kungiyar ta karrama ɗanjaridar ne yayin taron ƙaddamar da kalandar kungiyar ta shekerar 2025, da ya gudana a sakateriyar yan jaridu ta jihar Kano yau Alhamis.
Ahmad Hamisu Gwale dai ƙwararren ɗanjarida ne da ya ƙware wajen gabatar da shirye-shiryen wasanni kuma yana ɗaya daga cikin Masu gabatar da shirin ZAUREN WASANNI na tashar Premier Radio Kano Haka zalika shine mai magana da yawun kungiyar kwallon kafa ta BARAU FC.
Advertisements
