Sports
Ahmed Garba Yaro Yaro Ya Zama Sabon Mai Horar da Kano Pillars
DAGA MAIMUNA RABIU UMAR
Kungiyar Kano Pillars ta sanar da nada tsohon dan wasan Super Eagles da Borussia Dortmund, Ahmed Garba Yaro Yaro, a matsayin sabon mai horar da kungiyar.
Wannan mataki ya biyo bayan dakatar da tsohon kocin kungiyar, Usman Abdullah, sakamakon rashin kyakkyawan sakamako da kungiyar ke samu a wannan kakar wasa.
Mawallafin Jaridar NIGERIAN TRACKER Ya Zama Ma’ajin Kudi na Kungiyar Northern Online Media Group
Rashin nasara da Pillars ta yi da ci 4-1 a hannun Ikorodu United, tare da canjaras da Bayelsa United, ya haifar da gagarumin ce-ce-ku-ce a tsakanin magoya baya da shugabannin kungiyar, wanda hakan ya kai ga matakin sauya mai horarwa.
A cewar shugaban kungiyar, Alhaji Ali Nayara, Yaro Yaro – wanda tsohon dan wasan Kano Pillars ne – zai jagoranci kungiyar na wucin-gadi har sai kwamitin da aka kafa domin binciken Usman Abdullah ya kammala aikinsa, kafin a dauki matakin gaba.
