News
Mawallafin Jaridar NIGERIAN TRACKER Ya Zama Ma’ajin Kudi na Kungiyar Northern Online Media Group
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar kafofin watsa labarai na Yanar Gizo ta Northern Online Media Group ta zabi sabbin shugabannin Kungiyar a ranar Asabar.
Zaben da aka gudanar a Kaduna, a Arewa House, an yi shi ne karkashin kulawar kwamitin zabe na kungiyar.
Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu bakin gilas shiga harabarsa
Comrade Musa Mohammed daga jihar Kaduna ya zama sabon Shugaban ƙungiyar bayan da ya samu kuri’u 287, inda ya kayar da abokin takararsa, Comrade Lynn Adda, tsohon shugaban NUJ na Jihar Taraba, wanda ya samu kuri’u 138.
Comrade Femi Adi daga jihar Kogi ya lashe kujerar Sakataren Ƙungiyar da kuri’u 210, inda ya doke Comrade Rayyan Al-Hassan, wanda ya samu kuri’u 207.
A cewar kundin tsarin mulkin kungiyar, mukaman Mataimakin Sakataren ƙungiyar yana zuwa ne ga wadanda suka zo na biyu a takarar mukaman da suka tsaya. Saboda haka, Comrade Lynn Adda ya zama Mataimakin Shugaban ƙungiyar, yayin da Comrade Rayyan Al-Hassan ya zama Mataimakin Sakataren ƙungiyar.
Sauran shugabannin da suka fito ba tare da hamayya ba sun hada da:
Comrade Zaharaddeen Ishaq Zailani – Sakataren Kudi
Comrade Abraham Suleman – Mataimakin Sakataren Kudi
Comrade Abbas Yusha’u Yusuf – Ma’aji
A cikin jawabin godiya da ya gabatar, Comrade Musa Mohammed ya bukaci mambobin kungiyar a jihohi 19 na Arewa da su yi amfani da dandamalin sada zumunta don yaki da labaran karya tare da inganta nagartacciyar shugabanci.
A cewarsa, kafofin sada zumunta za su zama abin dogaro wajen watsa labarai ne kawai idan kwararrun ‘yan jarida suka karbe su tare da amfani da su ta hanyoyin da suka dace.
Amma abun farin ciki shi ne kwararrun ‘yan jarida suna karbar ragamar harkar yanzu,” in ji shi.
Ya bukaci mambobin kungiyar da su yi aiki bisa ka’idojin aikin jarida, tare da jaddada aniyarsa ta tabbatar da hadin kai da ci gaban kungiyar a cikin wa’adin mulkinsa na shekaru uku.
Daga karshe, ya godewa duk mambobin da suka halarci zaben, yana mai yin addu’a don samun dawowarsu lafiya zuwa gidajensu.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
