News
Mazauna Rimin Zakara Sun Yi Zanga-Zanga Kan Rushe Musu Gidaje Da Kwangaye
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mazauna Unguwar Rimin Zakara da ke Karamar Hukumar Ungoggo a Jihar Kano sun numa matukar damuwa da abin da ya faru a Unguwar ,inda aka zargi wasu jami’an tsaro tare da motocin rushe gurare da hallara a yankin, inda suka rushe gidaje da kwangaye.
Wannan mataki ya janyo bacin rai daga mazauna yankin, lamarin da ya haddasa tashin hankali har ya kai ga kone gidan mai gari, wanda al’ummar unguwar suka zarga da hannu a lamarin.
Ahmed Garba Yaro Yaro Ya Zama Sabon Mai Horar da Kano Pillars
Rahotanni sun nuna cewa an harbi mutane shida yayin rikicin, sannan an yi jana’izar mutane biyu. Wannan lamari ya tayar da hankalin al’umma, kuma har yanzu ba a samu cikakken bayani daga rundunar ‘yan sandan Jihar Kano kan batun ba.
EXPRESS RADIO ta ruwaito cewa Mazauna Unguwar sun kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiya da tabbatar da adalci ga al’ummar yankin.
Haka kuma, Sun kira da a kwantar da hankula tare da bin doka da oda domin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
