Connect with us

News

‎Hukumar Hisbah Ta Ceto Ƙananan Yara Mata 16 Daga Hannun Masu Fataucin Mutane A Kano. ‎ ‎

Published

on

Hukumar Hisbah Haramta Zancen Dare A Mota A Kano

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Jami’an Hisbah na Jihar Kano aikin da suka gudanar kwanan nan ya kai ga ceton ƙananan yara mata 16 da ake fataucin su zuwa ƙasashen waje.

Advertisement

‎An kama yaran ne a tashar mota ta Unguwa Uku a Kano, inda aka same su suna shiga cikin wata mota da za ta tafi Lagos.

Karin Kashi 50% Na Farashin Data Da Na Kiran Waya Zai Kayo Cikas Ga Tsarin Koyo Da Koyarwa —Dalibai

‎A cewar Mataimakin Kwamandan Hisbah, Mujahid Aminuddeen , yaran zasu nufi ƙasar Benin da Ghana, inda za a yi amfani da su. “Jami’anmu a tashar motar sun kama waɗannan yara ƙanana, ,” in ji Aminuddeen.

Advertisement

‎Aminuddeen ya yi kira ga iyaye su kula sosai da lafiyar ‘ya’yansu fiye da neman abin duniya. “Abin mamaki ne yadda wasu mutane ke son biyan kuɗaɗe masu yawa don a fatauci su, duk da haɗarin fyade, cin zarafi, har ma da mutuwa,” in ji shi.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending