News
Jami’an Hisbah Sun Kama Wadanda Suka Shirya Taron Casu Na Bankwana Da Shaidan A Kano
Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta kama mata shida da maza uku bisa zargin shirya taron casu da suka kira na bankwana da Shaidan yayin da ake shirin shiga watan Azumin Ramadana a wani shiri da suka gudanar mai taken Operation Ramadan Karim.
Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah a Jihar Kano, Dakta Mujahid Aminuddeen, ne ya bayyana hakan.
Little Ya Jajantawa Yan Kasuwar Singa Bisa Ibtila’in Gobara
Ya ce matasan sun shirya taron casu tare da gayyatar wasu fitsararrun mawaƙa masu yaɗa baɗala domin raƙashewa da sunan suna bankwana da Shaiɗan, lamarin da ya sabawa ka’idojin tarbiyya da doka a jihar Kano.
Ya kara da cewa da zarar an kammala bincike a kansu za a gurfanar da su a gaban Kotu.
Ya kuma bukaci al’umma su ci gaba da sa ido tare da bai wa hukumar rahoton duk wani abu da suka gani da ya saba wa tarbiyya ko doka.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
