Connect with us

News

Hisbah Ta Karyata Labarin Kama Shugaban Karamar Hukuma Da Yara A Kano 

Published

on

Hukumar Hisbah Haramta Zancen Dare A Mota A Kano

Hukumar Hisbah a Kano ta musanta rahotannin da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke cewa ta kama wani shugaban ƙaramar hukuma tare da wasu yara a wani otal.

A wata sanarwa da Mataimakin Kwamandan Hukumar, Dakta Mujahid Aminuddeen, ya fitar, ya bayyana cewa an karkatar da maganarsa ne, inda aka danganta masa abin da bai faɗa ba.

Jarumin Nollywood ya soki Seyi Tinubu kan mayar da hankali ga sake zaɓen mahaifinsa duk da halin ƙunci da ƴan Nijeriya ke ciki 

Ya ce ainihin abin da ya bayyana shi ne wani shugaban ƙaramar hukuma ya kai rahoto ga hukumar, tare da bayar da gudunmawa wajen kama wasu yara da aka gano ana kai su wani otal.

Dakta Mujahid ya ƙara da cewa ya yi kira ne ga sauran shugabanni da su yi koyi da irin wannan mataki na bayar da haɗin kai da jami’an tsaro domin dakile ayyukan da ba su dace ba.

Hukumar ta kuma buƙaci duk wanda ya yaɗa labarin da ke cewa an kama shugaban ƙaramar hukuma da yara a otal da ya janye shi ko kuma ya gabatar da hujjojin da ke tabbatar da hakan.

Advertisement

Hisbah ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauki matakin doka kan masu yaɗa labaran ƙarya da ke iya haddasa rudani a cikin al’umma.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending