Connect with us

News

Wani Matashi Ya Amsa Laifin Kashe Mahaifiyarsa Saboda Ta Ƙi Masa Wanka

Published

on

Wani mutum mai shekaru 30, Ofobuike Damian, ya gurfana a gaban Kotun Majistare ta 2 da ke Abakaliki bisa zargin kashe mahaifiyarsa da wuka bayan ta ƙi masa wanka.

Ana tuhumar Damian da laifi guda na kisan kai, inda ya amsa laifin a gaban kotu.

Hisbah Ta Karyata Labarin Kama Shugaban Karamar Hukuma Da Yara A Kano 

Mai gabatar da ƙara, David Njoku, babban lauya a gwamnatin jihar, ya shaida wa kotu cewa wanda ake ƙarar ya aikata laifin ne a ranar 19 ga Maris a yankin Ohatekwe, Ukawu da ke ƙaramar hukumar Onicha a Jihar Ebonyi.

Ya bayyana cewa Damian ya kashe mahaifiyarsa, Onyema Damian, ta hanyar soka mata wuka a baya, wanda ya yi sanadin mutuwarta.

Njoku ya ƙara da cewa laifin na da hukunci a ƙarƙashin sashe na 319 na kundin dokar laifuka na Jihar Ebonyi ta shekarar 2009.

Advertisement

Wanda ake tuhuma, wanda ba shi da lauya, ya shaida wa kotu cewa ya kashe mahaifiyarsa ne saboda ta ƙi masa wanka.

“Ban san yadda abin ya faru ba sosai, amma na tuna cewa na kashe ta ne saboda ta ƙi yi mini wanka,” in ji shi.

Babban Majistare, Chinedu Agama, ya bayar da umarnin tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali, yana mai cewa kotunsa ba ta da hurumin sauraron shari’ar kisan kai.

Haka kuma ya umurci a miƙa kundin shari’ar da hujjoji ga Sashen Lauyoyin Gwamnati (DPP) domin ba da shawara, tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 9 ga Afrilu domin ci gaba da ambato.

 

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending