News
Karin Kashi 50% Na Farashin Data Da Na Kiran Waya Zai Kayo Cikas Ga Tsarin Koyo Da Koyarwa —Dalibai
DAFA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Dalibai a Najeriya sun yi kira da a duba batun karin harajin kashi 50% na farashin data da na kiran waya saboda matsalar tattalin arziki da ake fama da ita.
Dalibai a jihar Enugu sun ce ayyukan sadarwa, kamar sabis na yanar gizo ya inganta harkar koyo da koyarwa yarma da bincike .
Masu Kallo Sun Nemi Mai Shadda Ya Sallami Fiddausi Yahya Daga Shirin Jamilu Jidda
Dan haka kara harajin kashi 50% na farashin data da na kiran waya zai kawo cikas ga tsarin binciki, koyo da koyarwa.
Daliban sun bayyana hakan ne ya yin zantawar su da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).
Mista Divine Eze, dalibin dake karantar tsarin kula da Muhalli a Jami’ar Najeriya Enugu Campus (UNEC), ya bukaci Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) da kamfanonin sadarwa da su janye batun karin harajin.
