News
Yadda daliban jami’a uku suka rasu a sakamakon turmutsitsin rige-rigen amsar tallafin shinkafa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wasu dalibai uku dake karatu a Jami’ar jihar Nasarawa dake Keffi sun gamu da ajalinsu a dalilin turmutsitsin amsar tallafin shinkafa da gwamnatin jihar ta bada domin raba wa dalibai ranar Juma’a.
Premium Times ta ruwaito cewa turmutsitsin ta faru ne bayan an tara buhunan shinkafan a filin taron yaye dalibai na Jami’ar inda ake jiran zuwan gwamnan jihar Abdullahi Sule kafin a fara rabawa.
Amurka Ta Ce Ba Ta Samu Wata Bukata A Hukumance Daga Gwamnatin Mulkin Sojan Nijar Na Ficewar Ta Ba
Wani dalibin jami’ar Moses Ajah ya ce dalibai sun tunkude jami’an tsaro dake gadin shinkafan suka yi wa tarin buhunan shinkafar ‘Alkafiar’ kowa ya fizgi rabonsa.
A yayin haka ke aka rika murkushe wasu.
” Tun kafin a fara rabon dalibai suka haura wurin da buhunan shinkafar suka kowa ya na suntumar buhu yana waskewa a guje. A yayain haka ne fa aka rika murkushe wasu, wasu kuma aka rika murje su da karfi tsiya.
Ajah ya ce ya ga yadda dalibai ke jidan buhunan shinkafa suna rugawa da shi dakunan su na zama a ciki da wajen jami’ar kafin gwamnan ya zo.
A lokacin da aka rubuta wannan labarin jami’an tsaro sun kwato buhunan shinkafan daga hannun wasu daliban.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
