News
Amurka Ta Ce Ba Ta Samu Wata Bukata A Hukumance Daga Gwamnatin Mulkin Sojan Nijar Na Ficewar Ta Ba
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata babban jami’ar ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta shaidawa Majalisar a ranar Alhamis cewa, Amurka ba ta samu wata bukata a hukumance daga gwamnatin Nijar na ficewa daga kasar ba.
Celeste Wallander, mataimakiyar sakataren tsaro kan harkokin tsaro na kasa da kasa, ta shaidawa kwamitin kula da ayyukan soji na Majalisar cewa, ya zuwa yanzu, gwamnatin mulkin sojan Nijar da aka fi sani da CNSP, ba ta nemi sojojin Amurka da su fice a hukumance ba.
Muna Kokarin Ganin An Shawo Kan Matsalar Ruwa A Asibitin Kwararru na Murtala – Dr Nagoda
Muryar Amurka ta ruwaito cewa Wallander ta ce, CNSP ya ce matsayin yarjejeniyar dakaru, wanda ya gindaya sharuddan kasancewar sojojin Amurka a wata kasa, yanzu ba shi da amfani. Sai dai, ta ce gwamnatin mulkin sojan ta “tabbatar mana da cewa, sojojin Amurka suna da kariya kuma ba za su dauki matakin da zai jefa su cikin hadari ba.”
Sojojin Amurka dai na da dakaru kusan 650 da kuma wasu daruruwa masu bayar da tallafi har yanzu a Nijar, wadda a baya ta kasance cibiyar yaki da ta’addanci. Sai dai a watan Yulin da ya gabata wasu sojojin Nijar sun hambarar da zababben shugaban kasar sannan bayan watanni suka nemi sojojin Faransa da su fice daga kasar.
Wallander ta ce Amurka na ci gaba da duba hanyoyin da za a bi wajen gudanar da ayyukan yaki da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a yankin.
A jamhuriyar Nijar, ma’aikatan Amurka sun maida dakarunsu a sansani daya, kuma suna ci gaba da gudanar da ayyukan jirage marasa matuki, amma iyakan aikinsu kariya ne kacal, in ji mataimakin sakatariyar yada labarai na Pentagon Sabrina Singh.
“Ana ci gaba da tattaunawa tare da CNSP don a samu hanyar ci gaba,” in ji Singh.
Shugaban Rundunar Sojojin Amurka a Afirka Janar Michael Langley, ya ce rashin fahimtar juna ya taka rawar gani sosai a Nijar da ma gwamnatoci da dama da aka yi wa juyin mulki a yankin Sahel a shekarun baya-bayan nan.
-
News5 days ago
Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026
-
News2 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News1 day ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
