Connect with us

News

Yan Sanda Sun Cafke Mutane 14 Da Ake Zargin Da Kashe  Ɗalibi A Jami’ar Gombe

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Rundunar ‘yan sanda ta kama wasu mutane 14 da ake zargi da hannu a rikicin da ya barke a wata jami’a a jihar Gombe.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa Abdussamad Musa dalibin dake matakin aji biyu a jami’ar a fannin ilimin laifuka da tsaro a jami’ar.

A Kan ₦500:  An Aike Da Ɗan Shekara 67 Gidan Yari Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Mata 2 Fyaɗe  A Bauchi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Buhari Abdullahi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, a ranar Juma’a, cewa akwai wasu mutane hudu da ake zargi da hannu a dumu-dumu a kan kisan wasu ɗalibai.

Advertisement

Lamarin, wanda ya samo asali ne sanadiyyar musu a kan kwallon kafa, ya faru ne a wajen harabar makarantar a daren ranar Talata. Ya ce an gano wukar da aka yi amfani da ita wajen aikata kisan.

Ya shawarci matasa da mazauna jihar da su kula da tattaunawar da suke yi a bainar jama’a, ya kuma kara da cewa duk wata tattaunawa da za a yi cikin tashin hankali ya kamata a guji.

Advertisement

“An yi wasan ƙwallon ƙafa ne don nishadantarwa ba don a kashe kowa ba, don haka mu guji cece-kuce da ka iya haifar da hargitsi da rigingimu musamman tsakanin matasa,” inji shi.

Kakakin Jami’ar, Janet Ibrahim, ta shaida wa NAN cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata da misalin karfe 7 na dare.

Advertisement

Misis Ibrahim ta ce lamarin ya faru ne sakamakon wata ‘yar rashin jituwa tsakanin kungiyoyi biyu bayan wasan kwallon kafa a wajen harabar makarantar.

Ta ce da farko dai an warware matsalar cikin ruwan sanyi, amma daga baya sauran kungiyar suka kai hari a harabar da marigayin ke zaune inda suka yi artabu.

Advertisement

“Hakan ya yi sanadin daba wa marigayin wuka a wuyansa, sannan aka garzaya da shi babban asibitin Kashere, inda daga baya ya mutu sakamakon zubar jini da ya wuce kima kamar yadda wani likita ya tabbatar,” inji shi.

Ta ce an gayyaci iyayen ne a ranar Laraba kuma sun halarci jana’izar marigayin da misalin karfe biyu na rana.

Advertisement

A cewarta, tun daga lokacin al’amura sun koma ga al’ummar da abin ya shafa.

Mista Ibrahim ya ce cibiyar ba ta da iko kan abin

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending