Connect with us

News

Babbar Magana: Barawo Ya Sace Sadaki Ana Shirin Daurin Aure A Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wani barawo da ba a kai ga gano shi ba ya sace sadaki a aljihun wakilin Ango a yayin daurin aure a masallacin Juma’a na Usman Bin Affan dake Gadon Kaya.

Advertisement

Rahotanni na nuni da cewa babban limamin Masallacin, Sheikh Aliyu Yunus ya gano hakan yayin da aka bukaci wakilin Angon ya gabatar da Sadakin inda aka nemi kudin aka rasa.

Wata majiya mai tushe ta shaidawa Jaridar Nigerian Tracker cewa wakilin Angon ya bada hakuri inda ya nemi limamin ya daura auren tare da alkawarin kawo sadakin daga baya.

Advertisement

A addinin Musulunci dai an amince da daura aure yayin da aka bada Sadaki nan take ko a ka dau alkawarin bayarwa daga baya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending