Connect with us

News

Majalisar Wakilan Najeriya Ta Kaddamar Da Bincike Kan Naira Biliyan 1.5 Da Aka Ware A Ma’aikatar Mata

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Majalisar Wakilan Najeriya ta kaddamar da bincike kan Naira biliyan 1.5 da aka ware domin biyan ‘yan kwangila, amma ana zargin manyan jami’an ma’aikatar mata ta tarayya sun karkatar da makudan kudaden.

Advertisement

Kwamitin majalisar mai kula da harkokin mata ya fara gudanar da bincike a Abuja kan korafe-korafen da ‘yan kwangila suka yi kan rashin biyan kwangilolin da aka aiwatar.

Babbar Magana: Barawo Ya Sace Sadaki Ana Shirin Daurin Aure A Kano

Shugaban kwamitin Kafilat Ogbara, ya bayyana cewa ma’aikatar ta bullo da sabbin kwangiloli da ba a kama su a cikin kasafin kudin 2023 ba tare da karkatar da Naira biliyan 1.5 a matsayin kudaden tsofaffin ‘yan kwangila.

Advertisement

Ta kara da cewa ma’aikatar, yayin da take bin ‘yan kwangila, ta ba da sabbin kwangiloli a jihohi 15 na tarayya, wanda ta yi zargin ba a kama su a cikin kasafin kudin 2023 ba.

A cewarta, “ba a biya kudin ‘yan kwangila ba, an karkatar da kudi, to ta yaya kuke biyan wadannan ‘yan kwangilar”?

Advertisement

Ta ce akwai ci gaba da binciken ma’aikatar da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta yi kan fitar da kudaden da aka kashe a watan Nuwamba da Disambar 2023 zuwa Naira biliyan 1.5.

Wadanda suka shigar da karar, a cewar Ogbara sun kuma yi zargin cewa ma’aikatar ta sayi ababen hawa a barikin soji da ke Abuja.

Advertisement

Mista Aloy Ifeakandu, Daraktan Kudi da Gudanarwa a ma’aikatar, ya ce ya bi umarnin hukuma ne kawai daga manyansa, yana mai cewa bayanan suna nan.

NAN ta rawaito cewa ofishin Akanta Janar na kasa ya bayyana cewa an saki Naira biliyan 1.5 ga ma’aikatar.

Advertisement

A halin da ake ciki, kwamitin ya gayyaci ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohaneye da ya gurfana a gaban sa a ranar Talata, 9 ga watan Yuli.

Kwamitin ya kuma umurci ma’aikatar da ta dakatar da duk wasu ayyukan kwangila a shekarar 2024, “har sai an warware matsalar tare da neman a ba ‘yan matan Chibok asusu na musamman da kuma yarjejeniyar fahimtar juna kamar yadda NAN ta tabbatar.

Advertisement

 

 

Advertisement

Solacebase

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending