Connect with us

News

Dorinar Ruwa Sun Lalata Gonaki 17 Masu Fadin Hekta 14 A Gombe

Published

on

gonbe hippo atack

Akalla gonaki 17 da ke da fadin kusan hekta 14 ne wasu dorinar ruwa suka mamaye tare da lalata amfanin gona a daren ranar Talata a kauyen Hinna, da ke karamar hukumar Yamaltu/Deba a jihar Gombe.

Manoman da abin ya shafa sun shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa dorinar ruwan sun fito ne daga wani kogi da ke kusa da gonakinsu, inda suka lalata amfanin gona da suka kusa girbi. Sun ce lamarin ya jefa rayuwarsu cikin mawuyacin hali tare da haifar da barazana ga tsaron abinci a yankin.

Advertisement

Dakarun Soji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 12 A Sambisa Da Dutsen Mandara ‎

Shugaban manoman yankin, Zakari Ladan, ya bayyana hare-haren dorinar ruwan a matsayin abin takaici matuƙa, yana mai cewa wannan matsala ta dade tana addabar manoman yankin ba tare da samun isasshen dauki daga gwamnati ba.

Advertisement

Ya kiyasta asarar da aka tafka ta kai kusan Naira miliyan bakwai, inda ya ce an lalata amfanin gona da suka hada da masara, shinkafa, tumatir, barkono, kuɓewa, karas da kuma kankana.

Ɗaya daga cikin manoman da abin ya shafa, Mohammed Zengina, ya ce ya yi asarar fiye da hekta 1.5 na gonar masararsa, wadda darajarta ta kai kimanin Naira 800,000 a cikin dare guda. Ya kara da cewa har yanzu bai farfado daga irin wannan barnar da ta taba faruwa a baya ba.

Advertisement

Haka kuma, manoman shinkafa a yankin sun koka da irin wannan barna duk da cewa sun tara kudade domin daukar mafarauta su rika tsaron gonakinsu daga dabbobin daji.

Da yake mayar da martani kan lamarin, Kwamishinan Noma na Jihar Gombe, Dakta Barnabas Malle, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta samu rahoton harin dorinar ruwan.

Advertisement

Ya ce an tura jami’ai domin tantance girman barnar, kuma za su mika rahoto ga Gwamna Inuwa Yahaya domin duba yiwuwar bayar da diyya ko taimakon gaggawa ga manoman da abin ya shafa.

Kwamishinan ya yi kira ga manoman da su kara hakuri, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar na daukar matakai domin magance matsalar tare da hana sake faruwarta nan gaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending