News
Kotu Ta Yanke Wa Dagaci Hukuncin Kisa A Gombe
Wata Babbar Kotu a Jihar Gombe, ta yanke wa Dagacin Gundumar Bangunji, Sulei Yerima, da Shedrack Aliyu Kwan hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun su da laifin aikata kisan kai.
Kotun mai lamba 8 da ke zamanta a Gombe, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Abdulsalam Mohammad, ta ce an same su da laifi ne bayan an tabbatar da tuhumar da ake yi musu.
Jami’an Yansanda Sun Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira
A hukuncin da ya yanke, alƙalin kotun ya kuma wanke tare da sallamar wasu mutum uku; Hamisu Ingila, Shanono Sarkin Pawa da Joseph Sarkin Noma, sakamakon rashin isassun hujjoji a kansu.
Tun da farko, an gurfanar da mutanen a gaban kotu ne, bisa laifukan haɗa baki, tayar da hankali, jikkata mutum, da kisan kai.
Laifukan da ake tuhumar su da su, sun saɓa wa dokar kundin Penal Code.
Ɓangaren masu gabatar da ƙara ya shaida wa kotun cewa a ranar 17 ga watan Agusta, 2017, a ƙauyen Biwula kusa da Bangunji a Ƙaramar Hukumar Shongom, waɗanda aka yankewa hukunci sun kai wani Shu’aibu Sale Galadima bari.
Sun yi masa munanan raunuka, waɗanda suka sanadin mutuwarsa.
Rahotanni sun nuna cewar sun aikata laifin ne bisa umarnin Shedrack Aliyu Kwan, yayin da wani mutum mai suna Joshua Michael ya tsere bayan faruwar lamarin.
Lauyan gwamnati kuma mai gabatar da ƙara, Barista Haruna Yelma, ya bayyana cewa laifukan suna da hukunci mai tsauri a ƙarƙashin doka.
Dukkanin waɗanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin lokacin da aka karanta musu tuhumar.
A yayin shari’ar, ɓangaren masu ƙara ya gabatar da shaidu 10 da kuma wasu hujjoji.
Ɓangaren masu karewa kuwa, ƙarƙashin Barista Herbert Nnwoye, ya gabatar da shaidu shida.
Yayin yanke hukunci, Mai shari’a Mohammad, ya ce kotun ta duba dukkanin shaidu da hujjojin da aka gabatar, sannan ta gamsu cewa Sulei Yerima da Shedrack Aliyu Kwan sun aikata laifin kisan kai.
Sai dai kotun ta ce hujjojin da aka gabatar kan sauran mutum ukun ba su nuna suna da hannu wajen aikata laifin kai-tsaye ba, don haka ta wanke su.
A ƙarshe, kotun ta yanke wa Dagacin Bangunji, Sulei Yerima, da Shedrack Aliyu Kwan hukuncin kisa ta hanyar rataya.
