News
Wata Babbar Mota Ta Yi Ajalin Mutum 3, Ta Jikkata 40 A Yobe
Mutane uku sun mutu, yayin da kimanin mutum 40 suka jikkata, sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a kan babbar hanyar Gombe zuwa Potiskum, a Jihar Yobe, arewacin Najeriya.
Lamarin ya auku ne da misalin karfe 2:30 na rana a ranar Laraba, kusa da garin Badejo, a ƙaramar hukumar Potiskum, bayan da wata babbar mota ɗauke da kaya ta ƙwace daga hannun direbanta ta afka cikin mutanen da ke zaune a gefen hanya.
Matakan Da Gwamna Abba Ya Ɗauka Kan Kisan Gillar Mata Da ‘Ya’yanta 6 A Kano
Wasu shaidu sun shaida wa LEADSHIP cewa, motar na tafiya ne da gudu mai yawa, lamarin da ya sa direban ya kasa sarrafa ta, ta kuma yi kan mutane da dama.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) reshen Jihar Yobe, Paul Andrew, ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda ya ce an kai waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci domin samun kulawa.
A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa cunkoson kaya fiye da ƙa’ida da kuma gudu mara misali na daga cikin abubuwan da suka haddasa hatsarin.
Hukumar FRSC ta sake jan hankalin direbobi da su riƙa bin dokokin hanya, musamman direbobin manyan motoci, domin rage yawaitar hatsurran da ke hallaka rayukan jama’a.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
