News
Kotun Koli Ta Kawo Ƙarshen Shari’ar Kisan Kudirat Abiola
Kotun Koli ta Nijeriya, a ranar Alhamis, ta yi watsi da ƙarar da gwamnatin Jihar Legas ta shigar dangane da shari’ar kisan Alhaja Kudirat Abiola, tare da tabbatar da sallamar tsohon Babban Jami’in Tsaron fadar shugaban mulkin soja, Major Hamza Al-Mustapha (mai ritaya).
Alhaja Kudirat Abiola, matar marigayi Cif M.K.O. Abiola—wanda ake ganin shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 1993—ta rasa ranta ne a Legas a lokacin zanga-zangar da ta biyo bayan soke sakamakon zaɓen.
Wata Babbar Mota Ta Yi Ajalin Mutum 3, Ta Jikkata 40 A Yobe
An zargi Hamza Al-Mustapha, wanda ya taɓa zama Chief Security Officer (CSO) ga marigayi Janar Sani Abacha, da hannu a kisan, tare da Mohammed Abacha da Lateef Shofolahan. An gurfanar da su a gaban Babbar Kotun Jihar Legas bisa tuhume-tuhume biyu da suka shafi haɗin kai wajen aikata kisa da kuma kisan Kudirat Abiola a ranar 4 ga Yuni, 1996.
A ranar 30 ga Janairu, 2012, Babbar Kotun Jihar Legas ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Moji Dada ta same su da laifi tare da yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya. Sai dai Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke hukuncin a ranar 12 ga Yuli, 2013, tana mai cewa ɓangaren masu gabatar da ƙara bai gabatar da hujjojin da suka isa tabbatar da laifi ba.
Daga bisani, gwamnatin Jihar Legas ta ɗaukaka ƙarar zuwa Kotun Koli, tana neman a dawo da hukuncin kisa. A shekarar 2014, Kotun Koli ta ba jihar izinin sake buɗe ƙarar duk da wucewar wa’adin shigar da ƙara.
Sai dai a zaman da aka yi a wannan mako, Kotun Koli ta bayyana cewa gwamnatin Jihar Legas ba ta gabatar da wata takarda ko kuma ta wakilta kanta da lauya ba tun bayan samun izinin sake buɗe shari’ar.
A hukuncin da kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Uwani Aba-Aji ya yanke, Kotun Koli ta ce hakan na nuni da rashin sha’awar ci gaba da shari’ar. Don haka Kotun ta yanke shawarar yin watsi da ƙarar gaba ɗaya tare da tabbatar da sallamar Hamza Al-Mustapha.
