Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 12 A Sambisa Da Dutsen Mandara ‎

Published

on

IMG 20251213 WA0008

Sojojin Najeriya da ke ƙarƙashin Rundunar Aikin Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, sun ce sun hallaka ’yan ta’adda 12 na Boko Haram da ISWAP a wasu hare-hare da suka kai a Dajin Sambisa da yankin Dutsen Mandara.

‎A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce farmakin ya gudana ne a ranar 22 ga Janairu, 2026, lokacin da ’yan ta’addar suka yi yunƙurin kai wa dakarun kwanton bauna ta amfani da bama-baman gefen hanya da harbin bindiga.

Dakarun Soji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 12 A Sambisa Da Dutsen Mandara ‎

‎Sanarwar ta ce dakarun Sector 1 sun mayar da martani, inda suka kashe ’yan ta’adda 10 ciki har da wasu manyan kwamandoji biyu da aka bayyana sunayensu Basulhu da Ubaida.

‎Bayan haka, sojojin sun ci gaba da bincike a yankin, inda suka kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku, bindiga mai harbi ɗaya, babura biyar, gurneti guda biyu, na’urorin sadarwa da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen kera bama-bamai.

‎A wani farmaki na daban da aka kai a yankin Malkube, rundunar ta ce ta sake hallaka ’yan ta’adda biyu, ba tare da an samu asarar rai a ɓangaren sojoji ba, tare da kwato ƙarin makamai da kayayyakin sadarwa.

Advertisement

‎Haka kuma, rundunar ta ce a safiyar ranar, wasu dakarunta sun hana ’yan ta’adda shiga Najeriya daga ƙasar Kamaru ta yankin Galakura, inda suka tilasta musu guduwa tare da barin babura da wasu kayayyaki a baya.

‎Rundunar sojin ta ce za ta ci gaba da matsa lamba a kan ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas, domin hana su sake samun damar kai hare-hare.

‎Sanarwar ta fito ne daga Laftanar Kanar Sani Uba, jami’in yaɗa labarai na Hedikwatar Rundunar Aikin Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas.

 

 

PRNIGERIA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending