News
Masu Kallo Sun Nemi Mai Shadda Ya Sallami Fiddausi Yahya Daga Shirin Jamilu Jidda
Masu kallo daga lunguna da sako daban-daban sun fito suna me bayyana ra’ayoyin su game da sabon shiri mai dogon zango mai suna Jamilu Jidda wanda Furodusa Abubakar Bashir Mai Shadda ya shirya kuma ake haskawa a tashar Arewa 24.
Shidai wannan shiri an shirya shi ne akan rayuwar wasu mutane da tsantsar boko ta ratsa.
Yajin Aikin Likitoci Ya Tsayar Da Al’amura A Asibitocin Abuja
Sai dai a nasu ra’ayin Yan kallon suna ganin cewa rawar da aka ba jaruma Fiddausi Yahya a shirin a matsayin wacce tafito daga gidan boko sam bai karbeta ba duba da yadda turanci yayi karanci a bakinta.
Ra’ayoyi daban daban daga yan kallo sun cika shafukan sada zumunta inda mutane da yawa ke ganin cewa ya kamata ace jarumar da ta hau wannan rawar ta kasance mai iya turanci yar boko sosai,Har wasu daga ciki na ambaton wasu jarumai suna nuna cewar sune ya dace su hau wannan shiri.
Ga kadan daga cikin ra’ayoyin mutane
Jibril Dawud Musa yace ”Ku dauko Maryam both ko Rahama Sadau”
Dalhatu Lawal ”Maganar gaskia bata dace da role din da aka bata ba saboda ya kamata ace yar gidan farfesa a ji turanci ya kama bakin ta kamar yadda akaji maman ta da kanwarta suna yi”.
Abubakar sadeek yace ” Haba ai kamata ya yi ace Maryam both aka dauko”
Ni’ima Usman ” Wallahi Maryam Labarina tafi dacewa saboda tafi iya turanci.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News6 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
