News
Yajin Aikin Likitoci Sun Tsayar Da Al’amura A Asibitocin Abuja
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Likitoci masu neman ƙwarewa a Abuja sun fara yajin aiki saboda rashin biyan albashi, kuɗaɗen alawus, da sauran haƙƙoƙinsu.
A taron manema labarai da ƙungiyar likitocin ta gudanar a ranar Laraba, shugaban ƙungiyar, Dokta George Ebong, ya bayyana cewa yajin aikin na gargaɗi ne kuma zai ɗauki kwanaki uku.
NCDC Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 22, 143 Sun Kamu Cikin Mako 2 Sakamakon cutar Zazzaɓin Lassa
Yajin aikin ya shafi ayyukan asibitocin gwamnati a babban birnin tarayya, inda aka samu cikas a ayyukan jinya.
Dokta Ebong ya bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne bayan wa’adin makonni uku da suka bai wa gwamnati don warware matsalolin bai haifar da sakamako ba.
Ƙungiyar likitocin ta koka kan halin ko-in-kula da asibitocin Abuja ke ciki, inda suka nemi Ministan Abuja, Nyesome Wike, da ya shiga cikin lamarin don magance matsalar kafin yajin aikin ya tsawaita.
A ranar Talata ne shugabannin ƙungiyar suka cimma matsayar shiga yajin aiki bayan wani muhimmin taro da suka gudanar.
-
News6 days ago
Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026
-
News3 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News2 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
