Sports
AN RABA MAKI TSAKANIN KUNGIYAR REAL MADRID DA ATLETICO MADRID
DAGA UMAR ABDULLAHI HOTORO
Real Madrid da Atletico Madrid sun tashi 1-1 a gasar La Liga, karawar mako na 23 da suka fafata a wasan hamayya ranar Asabar a filin Santiago Bernabeu.
Atletico Madrid ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Julian Alvarez a bugun fenariti tun kafin hutu, inda suka tafi hutun rabin lokaci da ci 1-0. Sai dai daga baya Real Madrid ta farke ta hannun Kylian Mbappe, wanda ya ci ƙwallo ta 23 a kakar bana a duka gasa da ya buga wa Madrid.
Wannan shi ne karo na biyu da suka kece raini a wannan kakar, bayan sun tashi 1-1 a wasan farko da suka buga a ranar 29 ga watan Satumba.
Shi ne karon farko da aka buga wasan hamayyar Madrid a 2025, kuma na farko da Kylian Mbappe ya taka leda a irin wannan fafatawa.
Da wannan sakamakon, Real Madrid ce ke kan gaba a teburin La Liga da tazarar maki ɗaya tsakaninta da Atletico Madrid wadda ke da maki 49 a matsayi na biyu.
Za a sake ganin Real Madrid a fagen wasa ranar Talata 11 ga watan Fabrairu, inda za ta kara da Manchester City a wasan cike gurbi na Kofin Zakarun Turai. Ita kuwa Atletico Madrid za ta karɓi bakuncin Celta Vigo a gasar La Liga ranar Asabar 15 ga watan Fabrairu.
