News
INEC Ta Fitar Da Ranar Gudanar Da Zabukan Cike Gurbi A Jihohi 12
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana ranar 16 ga watan Agusta, 2025 a matsayin ranar da za a gudanar da zabukan cike gurbi a mazabu 16 da ke cikin jihohi 12 a fadin Najeriya.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin taron tuntuba karo na biyu tsakanin hukumar da shugabannin jam’iyyun siyasa, wanda aka gudanar a birnin tarayya Abuja.
Shugaba Tinubu Ya Ƙi Sanya Hannu Kan Ƙudurin Sauya Dokar NDLEA
Farfesa Mahmood ya bayyana cewa zabukan cike gurbin za su shafi kananan hukumomi 32, da gundumomi 356 tare da rumfunan zabe guda 6,987.
Ya kara da cewa jimillar masu kada kuri’a da za su shiga wannan zabe sun kai 3,553,659, wadanda suka yi rajista a wuraren da za a gudanar da zabukan.
INEC ta ce za ta ci gaba da tuntubar jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da an gudanar da sahihin zabe cikin lumana da gaskiya.
