Connect with us

News

Farm Centre: Gwamnatin Kano Ta Ce Ba Ta Taɓa Hana Kowanne Ɗan Ƙasa Ko Ƙungiya Bayar da Gudummawa Ba

Published

on

1750963672499704 0

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ba ta taɓa hana kowanne ɗan ƙasa ko wata ƙungiya bayar da gudummawa ga ’yan kasuwar Farm Centre da gobara ta shafa ba.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 26 ga Yuni, 2025.

INEC Ta Fitar Da Ranar Gudanar Da Zabukan Cike Gurbi A Jihohi 12

Waiya ya ce gwamnatin ta buɗe asusun tallafi na musamman tare da kafa wani kwamiti domin tabbatar da cewa duk gudummawar da jama’a da kungiyoyi ke bayarwa za ta isa hannun waɗanda lamarin ya shafa kai tsaye, ba tare da wata tangarda ko karkatar da kayan tallafi ba.

Kwamishinan ya ce gwamnati tana da niyyar gudanar da aikin sake gina kasuwar cikin gaggawa, domin dawo da rayuwar kasuwanci a yankin.

“Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da kashe fiye da naira biliyan biyu domin aikin sake gina kasuwar, fadada ta, kafa cibiyar kashe gobara da kuma samar da hasken tituna domin inganta tsaro da lafiyar muhalli,” in ji Waiya.

Gwamnatin Kano ta kuma ce tana maraba da kowace gudummawa daga cikin gida ko waje, tare da tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon tallafin.

Advertisement

Wannan bayani ya zo ne a yayin da ake ci gaba da samun raɗe-raɗi a kafafen sada zumunta da ke nuna cewa gwamnatin jihar ta hana jama’a bayar da gudummawa ga waɗanda gobarar ta shafa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending