News
Shugaba Tinubu Ya Ƙi Sanya Hannu Kan Ƙudurin Sauya Dokar NDLEA
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙi amincewa da ƙudurin dokar sauya tsarin hukumar hana fatauci da sha da miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, wato NDLEA, na shekarar 2025.
A wata wasika da Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Tajudeen Abbas, ya karanta a zaman majalisar ranar Alhamis, shugaban ƙasar ya bayyana dalilan da suka sa ya ƙi sanya hannu kan dokar.
An Kama Mace Da Wasu Mutane Uku Bisa Zargin Kwacen Baburan Adaidaita Sahu A Kano
Ƙudurin dokar dai ya nemi bai wa hukumar NDLEA damar riƙe wani kaso daga cikin kuɗaɗen da ake ƙwato daga miyagun ƙwayoyi da sauran laifukan da suka shafi fatauci.
Sai dai Shugaba Tinubu ya bayyana cewa wannan sabon tsarin ya saba wa dokokin da ke aiki a halin yanzu, musamman sashe na 58, ƙaramin sashe na 4 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.
Shugaban ya ce, bisa tsarin da ke aiki yanzu, duk wani kuɗi da aka samu daga laifukan kuɗi ya kamata a tura shi ne zuwa asusun Kadarori na Gwamnatin Tarayya.
Har wa yau, ƙin amincewar Shugaban ƙasar kan wannan kuduri na NDLEA na zama na biyu cikin mako guda da ya ƙi sanya hannu kan wata doka.
A farkon makon nan, a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya ƙi sanya hannu kan ƙudirin gyaran dokar Asusun Amintattu na Laburaren Majalisar Tarayya ta 2025, inda ya danganta ƙin amincewar da saɓani da manufofin gwamnati musamman a ɓangaren kula da kuɗaɗe da albashi.
Majiyar NAN ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na ƙoƙarin tabbatar da cewa duk wata doka da za ta shafi tsarin kuɗi ko amfani da kadarorin gwamnati ta bi ka’idojin da kundin tsarin mulki ya tanada.
