News
An Kama Mace Da Wasu Mutane Uku Bisa Zargin Kwacen Baburan Adaidaita Sahu A Kano
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta cafke mutane huɗu da ake zargi da aikata laifin kwacen baburan adaidaita sahu a sassa daban-daban na jihar.
Cikin waɗanda aka kama har da wata mace mai shekaru 25 mai suna Maryam Ibrahim, ‘yar asalin jihar Bauchi.
NLC Ta Yi Barazanar Rufe Abuja Bayan Tinubu Ya Kammala Kaddamar Da Ayyuka
Mukaddashin Kakakin rundunar, DSP Hussaini Abdullahi, ya shaida wa manema labarai cewa sauran mutanen da ake zargi sun haɗa da Auwal Mohammed mai shekaru 30 daga unguwar Hotoro, Muhammad Tujuddeen daga Kundila, da kuma Suleiman Lawan wanda aka fi sani da “Aljan” daga unguwar Sheka.
DSP Hussaini ya ce waɗanda ake zargin sun tare wani direban adaidaita sahu mai suna Shu’aibu Aliyu a karamar hukumar Kura, inda suka yi masa fashin babur ɗinsa.
Ya ƙara da cewa binciken da suka gudanar ya kai ga kama waɗanda ake zargi da karɓar sayen baburan da aka sace, tare da kwato babura guda shida da ake zargin satar su aka yi.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar na ci gaba da ƙoƙari wajen yaki da masu aikata laifuka, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
