Connect with us

News

NLC Ta Yi Barazanar Rufe Abuja Bayan Tinubu Ya Kammala Kaddamar Da Ayyuka

Published

on

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), reshen Babban Birnin Tarayya Abuja, ta ce tana shirye-shiryen rufe Abuja gaba ɗaya a matsayin martani ga jinkirin warware matsalolin ma’aikatan ƙananan hukumomi.

Shugaban ƙungiyar, Dr. Stephen Knabayi, ne ya bayyana hakan cikin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Alhamis, inda ya nuna cewa matakin zai biyo bayan kammala bikin ƙaddamar da ayyuka da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gudanar a ranar 3 ga watan Yuli, domin cika shekara biyu a kan mulki.

Yan Bindiga Sun Ƙwace Iko Da Jagorancin Ƙaramar Hukuma A Katsina

Dr. Knabayi ya ce matakin rufe Abuja gaba ɗaya wani salo ne na nuna rashin jin daɗi da jawo hankalin hukumomin Abuja kan dogon yajin aikin da ma’aikatan ƙananan hukumomi ke yi, wanda ya dade yana ci gaba ba tare da mafita ba.

Rahotanni sun bayyana cewa a halin yanzu cibiyoyin lafiya na matakin farko a FCT na ci gaba da kasancewa a rufe, yayin da malamai na makarantun firamare ke ci gaba da zaman gida. Haka kuma, ofisoshin ƙananan hukumomi guda shida a yankin sun kasance a rufe tun watanni da suka wuce.

Ma’aikatan sun shiga yajin aiki ne sakamakon kin biyan sabon mafi ƙanƙantar albashi da kuma ƙarin alawus na kashi 40 bisa ɗari da ake kira “Peculiar Allowance.”

Baya ga haka, akwai kuma matsalolin da suka haɗa da kin aiwatar da ƙarin albashi na kashi 25 zuwa 35 bisa ɗari, da kuma kin biyan alawus na Naira 35,000 da gwamnatin tarayya ta amince da shi a baya.

Advertisement

Dr. Knabayi ya bayyana takaicinsa kan yadda lamarin ya ki samun mafita, yana mai zargin shugabannin ƙananan hukumomi da nuna halin ko-in-kula da walwalar ma’aikatansu.

Ya bayyana cewa NLC ta bai wa gwamnatin FCT wa’adin kwanaki bakwai tun daga ranar 13 ga Yuni, domin warware matsalolin da ma’aikatan kiwon lafiya, malamai da sauran ma’aikatan ƙananan hukumomi ke fuskanta.

Wa’adin ya ƙare a ranar 20 ga Yuni, amma babu wani matakin warware matsalolin da aka ɗauka.

A cewar Knabayi, ƙungiyar ta dakatar da aiwatar da yajin aikin ne kawai domin ta ba Shugaba Tinubu damar kammala bukukuwan cika shekara biyu a mulki ba tare da tangarda ba.

“Amma yanzu da bukukuwan za su ƙare, babu wata mafita da gwamnati ta samar, za mu ɗauki matakin da ya kamata,” in ji shi.

Ya ce NLC ta riga ta sanar da hukumomin tsaro da na FCT game da shirin rufe birnin gaba ɗaya a matsayin matakin ƙarshe domin tilasta gwamnati biyan buƙatun ma’aikatan ƙananan hukumomi.

Advertisement

Har ila yau, Knabayi ya koka kan yadda aka fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 a watan Mayu, amma daga bisani aka dakatar da biyan albashin a watan Yuni ba tare da wani bayani ba.

Ya kuma zargi shugabannin ƙananan hukumomi da amfani da maƙudan kuɗaɗe wajen shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na babban birnin tarayya da ake sa ran yi a watan Fabrairun 2026.

A cewarsa, kuɗaɗen da ake kashewa kan shirye-shiryen zaɓen sun isa a biya dukkan buƙatun ma’aikatan da ke cikin yajin aiki.

Daga ƙarshe, ya roƙi Ministan Abuja, Nyesom Wike, da ya ɗauki matakin gaggawa domin tilasta shugabannin ƙananan hukumomi su warware matsalolin jin daɗin ma’aikatansu domin kaucewa rufe Abuja gaba ɗaya.

 

 

Advertisement

STALLION TIMES 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending