Connect with us

News

Tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi Ya Zargi Wasu Jiga-jigan Gwamnati Da Hana Sauya Tsarin Zabe

Published

on

Rotimi Amaechi
Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi,

Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya zargi wata ƙungiya mai ƙarfi a cikin gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari da hana aiwatar da sauye-sauyen tsarin zaɓe.

A yayin taron ƙasa kan gyaran tsarin zaɓe da ƙungiyar Movement for Credible Elections (MCE) ta shirya a Abuja, Amaechi ya ce Buhari ya yi ƙoƙari wajen inganta tsarin zaɓe, amma wasu manyan mutane a cikin gwamnatinsa sun hana hakan.

Advertisement

Asibitin Kwararru NaBest Choice Zasu Duba Masu Wasu Cututtuka Kyauta, Da Ragin Kaso 50% Ga Masu Aikin Tiyata.

Amaechi ya jaddada cewa ana iya samun sauyi na gaskiya ne kawai idan ‘yan ƙasa suka tashi tsaye, ba tare da dogaro da shugabanni ba.

Amaechi ya ce fitowar jama’a da yawa wajen zaɓe ita ce hanya mafi ƙarfi wajen hana magudi, yana mai cewa duk wanda ya ƙoƙarta canza sakamako ko cire takardun zaɓe zai jefa kansa cikin matsala.

Advertisement

Ya nuna rashin jin daɗinsa kan rashin halartar tsohon Shugaba Goodluck Jonathan da tsohon Sakataren Commonwealth, Emeka Anyaoku, waɗanda ake sa ran za su halarta.

Amaechi ya ce duk wani shawarwari daga taron ba za su yi tasiri ba sai ‘yan ƙasa sun nemi a ɗauki mataki.

Advertisement

A nata jawabin, tsohuwar Ministar Ilimi, Dr. Oby Ezekwesili, ta ce sahihin zaɓe shi ne ginshiƙin dimokuraɗiyya, tana mai cewa Najeriya ta gaza cika ƙa’idojin dimokuraɗiyya tun daga 1999.

Ta buƙaci a bai wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ikon gurfanar da masu laifin zaɓe domin tabbatar da gaskiya da inganta dimokuraɗiyya.

Advertisement

 

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending