News
Abin Takaici Ne Dalibi Ya Yi Shekaru A Aji, Amma Mara Ilimi Ya Samu Digiri A Rana Daya” — Inji Farfesa Jega
Tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) kuma shugaban hukumar gudanarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana matukar damuwa kan yadda wasu jami’o’in Najeriya ke raba digirin girmamawa ga mutanen da ba su da sahihin cancanta ta fannin ilimi.
Farfesa Jega ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a matsayin shugaban taro a laccar yaye dalibai karo na 14 na jami’ar Open University da ke Abuja, a ranar Juma’a 11 ga Afrilu, 2025.
NDLEA Ta Kama Mutane 22, Ta Kwato Miyagun Kwayoyi Da Makamai A Kano
“Abin takaici ne a ce dalibi ya kwashe shekaru hudu ko fiye yana karatu a aji, malamai kuma suna yin bincike da kokari wajen ciyar da ilimi gaba, amma daga karshe sai a ga jami’a tana ba wani da bai taba shiga aji ba digirin girmamawa,” in ji Jega.
Ya ce wannan dabi’a tana rage kimar ilimi da mutuncin jami’o’in kasar nan, kuma tana jefa tambaya kan sahihancin nasarorin da dalibai da malamai ke samu ta hanyar hakuri da jajircewa.
Jega ya yabawa daliban da suka kammala karatunsu tare da kira gare su da su ci gaba da sadaukar da kai domin farfado da martabar ilimi a Najeriya. Haka kuma ya bukaci malamai da ma’aikatan ilimi su dage wajen kare mutuncin sana’ar koyarwa da gujewa duk wata alaka da karrama mutanen da ba su cancanta ba saboda siyasa ko wata manufa ta kai-da-kai.
A nasa jawabin, shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB), Dr. Akinwumi Adesina, ya jinjinawa ci gaban da dalibai ke samu a Najeriya. Ya bayyana cewa a da, kasashen duniya na alfahari da ingancin ilimin Najeriya, kuma har yanzu wannan kima na nan, sai dai ya yi gargadi cewa siyasa na barazana ga cigaban da aka samu idan ba a dauki mataki ba.
