Connect with us

News

Kashi 91% Na ’Yan Najeriya Ba Su Amince Da Tinubu Ba ,Zai Yi Wuya Ya Kai Mataki Na Uku A 2027 — El-Rufaiai

Published

on

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa mafi yawan ’yan Najeriya ba su gamsu da salon mulkinsa ba, kuma samun nasara a zaɓen 2027 na iya kasancewa mai matuƙar wahala a gare shi.

El-Rufai ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin PRIMETIME na gidan talabijin na Arise News a daren Litinin, inda ya ce alkaluman Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) sun nuna cewa kusan kashi 91% na ’yan Najeriya ba su amince da gwamnatin Tinubu ba.

Advertisement

Matasa Sun Fara Jan Ragamar Yaki da Wariya Ga Masu Bukata Ta Musamman A Kano

“Wannan ba ra’ayina bane kawai. Hukumar NBS ce ta fitar da wannan alkaluma. Ni kuwa ina magana ne da hujjoji,” in ji El-Rufai.

Ya ce kamar yadda Tinubu ya auna gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan cikin shekara guda a 2012, to shima adalci ne a auna tasa gwamnatin bayan shekara biyu.

Advertisement

El-Rufai ya nuna damuwarsa kan yadda matsalolin tsaro ke ƙara ta’azzara a ƙasar, yana mai cewa gwamnatin tarayya ce ke da alhakin magance matsalar, ba gwamnoni jihohi ba.

“Tsaro na ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya ne. Shugaban ƙasa ne yakamata ya warware matsalar, ba wai a dora wa gwamnonin jihohi nauyin abin da ba ya hannunsu ba,” in ji shi.

Advertisement

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa bisa yadda abubuwa ke gudana, yana da wuya Shugaba Tinubu ya samu nasarar lashe zaɓen 2027.

“Na kalli alkaluma da yanayin siyasa. Idan aka ci gaba da tafiya haka, Tinubu zai yi sa’a idan ma ya zo na uku a 2027,” in ji El-Rufai.

Advertisement

Har zuwa yanzu, ba a samu wata martani daga fadar Shugaban Ƙasa ko jam’iyyar APC kan wannan kalamai na El-Rufai ba. Sai dai wannan ba shi ne karon farko da tsohon gwamnan ke sukar gwamnatin Tinubu ba — musamman a kan batutuwan tattalin arziki da rashin tsaro.

 

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending