News
An Kama Dan Sandan Bogi Dake Bayar Da Hannu A Kano
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da cafke wani matashi mai suna Nasiru Shitu, mai shekaru 33, mazaunin unguwar Kofar Waika, bisa zargin sanya kayan jami’an tsaro yana bayar da hannu a kan tituna tare da cutar da jama’a.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai jiya Litinin a Kano.
A cewar sanarwar, kama wanda ake zargin ya biyo bayan korafe-korafen da al’umma suka shigar, inda suka koka kan yadda wasu bata-gari ke amfani da kayan jami’an tsaro suna tsayawa a kan titi suna cutar mutane.
Kiyawa ya ce, “Bayan samun wadannan korafe-korafe, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin kara sanya ido a wuraren da ake zargin ana aikata wannan mummunan aiki.”
Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya amince da laifinsa, inda ya bayyana cewa yana shaye-shaye, kuma son aikin dan sanda ne ya sanya shi rika sanya kayan jami’an tsaro yana bayar da hannu a kan titi.
Rahoton ya kuma nuna cewa a baya an taba kama shi kan irin wannan laifi, aka gargade shi, amma ya ki hakura, har ma da iyayensa suka ja masa kunne kan ya daina amfani da kayan jami’an tsaro da ba shi da ikon amfani da su.
Rundunar ta tabbatar da cewa za a gurfanar da matashin a gaban kotu kan laifin yinsojan gona.
