News
An Sanya Dokar Hana Zirga-Zirga A Yauri
Gwamnatin Karamar Hukumar Yauri a Jihar Kebbi ta sanya dokar hana zirga-zirga daga ƙarfe 10 na dare zuwa 7 na safe, har tsawon kwanaki uku, bayan rikici tsakanin matasan Unguwar Tashar Kattai da wasu masu haƙar zinare wanda ya jawo asarar rayuka da lalacewar dukiya a garin.
Shugaban ƙaramar hukumar, Abubakar Shu’aibu (Ƙauran Yauri), ya bayyana wa manema labarai cewa rikicin ya fara ne ranar Asabar da ta gabata, lokacin da wasu masu haƙar zinare suka kai hari suka kashe mutum ɗaya, sai dangin mamacin suka ramawa a ranar Litinin. Rikicin ya ƙara ta’azzara yayin da wasu shaguna da babura suka kone cikin garin.
Shu’aibu ya ce sun nemi sunayen wadanda suka aikata kisan, wasu sun nuna aniyar bayar da haɗin kai, amma abokan su sun hana hakan. Saboda haka, ya tuntubi hukumomin tsaro da sojoji don dawo da zaman lafiya a Yauri.
Ya kara da cewa rikicin ya sake ta’azzara bayan mataimakinsa ya dawo daga jana’iza ya shaida masa cewa masu haƙar zinare suna kai hari ga mutane a cikin garin.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
