Connect with us

News

Mutum 6 Sun Mutu A Hadarin Jirgin Ruwa A Jigawa

Published

on

Jirgin Ruwa

Rundunar ’yan sanda a jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane shida – ciki har da kananan yara – a wani hadarin jirgin ruwa da ya afku a kauyen Zangwan Maje da ke karamar hukumar Taura.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Shi’isu Lawan Adam, ya fitar, ya ce hadarin Jirgin Ruwa  ya faru ne a ranar 27 ga watan Yuni, lokacin da yara 15 ke dawowa daga gona daga Jejin Gunka zuwa kauyensu na Zangwan Maje.

Advertisement

Me ya sa Man United ta haramta buga sunan Cristiano Ronaldo a jesinta?

Sai dai jirgin ruwan da suke ciki ya kife sakamakon cikar kaya fiye da ƙima, iska mai ƙarfi da kuma ambaliya da ta taso a lokacin.

“Rundunar ta samu kiran gaggawa, kuma aka tura jami’ai domin ceto rayuka,” in ji SP Shi’isu.

Advertisement

 

An ceto yara bakwai da ransu, yayin da aka gano gawarwakin yara mata biyu nan take. A ranar Talata da safe kuma, aka sake gano gawarwakin yara mata huɗu.

Advertisement

Likitoci a asibiti sun tabbatar da mutuwar yaran bayan an kai su cibiyar lafiya.

Kwamishinan ’yan sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ya mika ta’aziyya ga iyalan mamatan da kuma al’ummar yankin Zangwan Maje.

Advertisement

 

 

Advertisement

PRNIGERIAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending