News
Tsarin Fansho Na CPS Ya Jefa Tsofaffin ‘Yan Sanda Cikin Ƙunci —Kayode Egbetokun
Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya ce yawancin tsofaffin jami’an ’yan sanda da suka yi ritaya ƙarƙashin tsarin fansho na haɗin gwiwa wato Contributory Pension Scheme (CPS), na rayuwa cikin ƙunci da talauci, lamarin da ke haifar da fargaba a zukatan jami’an da ke aiki a yanzu.
Egbetokun ya bayyana hakan ne a wani taro da ya jagoranta tare da manyan jami’an ’yan sanda a Abuja ranar Talata.
CAC Ta Ba Kamfanoni 100,000 Wa’adin Watanni Uku Ko Ta Goge Sunayensu Daga Rajista
A cewarsa, yanayin da tsofaffin jami’an ke ciki ba zai karfafa gwiwar masu aikin yau ba, duba da irin sadaukarwar da waɗanda suka yi ritaya suka bayar wa ƙasa.
“Fargabar fadawa cikin talauci bayan ritaya ta bazu a tsakanin jami’ai, kuma hakan yana hana su natsuwa da himma wajen aiki,” in ji Egbetokun.
Ya ce duk da kokarin da ake yi na bayyana yadda tsarin CPS ke aiki ga jami’an, hakan ba ya rage matsaloli, illa ma ƙara dagula al’amura.
Sufeto Janar ya ce rundunar ta gabatar da ƙorafi a gaban Majalisar Tarayya a wani zaman sauraron ra’ayoyi, inda ake duba yiwuwar cire jami’an ’yan sanda daga tsarin CPS gaba ɗaya.
Ya ƙara da cewa, tuni aka bayyana hujjojin da ke nuna cewa tsarin ba ya amfani wa jami’an da suka bauta wa ƙasa tsawon shekaru.
Sufeto Janar Egbetokun ya maida martani kan zarge-zargen da wasu ke yi cewa yana adawa da ficewar ’yan sanda daga tsarin CPS, inda ya bayyana cewa hakan ba gaskiya ba ne.
“Ba ni da wani dalilin adawa da cire jami’an daga tsarin, musamman idan hakan zai inganta rayuwar su da na iyalansu bayan ritaya,” in ji shi.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
