Business
Ƴan Kasuwa Sun Ƙi Sauko Da Farashin Mai Duk Da Raguwar Sa A Kasuwar Duniya
Duk da raguwar farashin danyen mai a kasuwar duniya daga dala 130 zuwa dala 100 a kowace ganga, ’yan kasuwar mai a Najeriya sun ki rage farashin fetur, inda har yanzu ake sayar da shi a kan sama da ₦1,300 a kowace lita a sassa daban-daban na kasar kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito.
Rahotanni sun nuna cewa faduwar farashin danyen mai ya biyo bayan kyautata zaton cewa tattaunawar diflomasiyya tsakanin Amurka da Iran na iya sa man Iran ya koma kasuwannin Asiya nan gaba kadan.
Gwamnatin Tarraya Za Ta Ɓullo Da Lambar Tantance Ɗalibai Tun Daga Matakin Firamare
Sai dai binciken da aka gudanar a Legas da kewayenta ya nuna cewa gidajen mai ba su sauke farashin ba, duk da canjin da aka samu a kasuwar duniya.
Wasu gidajen mai sun sayar da fetur a kusan ₦1,333 a kowace lita, yayin da farashin daga wuraren ajiya ya kasance kusan ₦1,270 a kowace lita. Haka kuma, matatar Dangote ta sanya nata farashin a kusan ₦1,285 a kowace lita.
A babban birnin tarayya, Abuja, farashin ya ci gaba da kasancewa mai tsada, inda ake sayar da fetur har zuwa ₦1,371 a kowace lita, duk da shafe sa’o’i 24 da faduwar farashin danyen mai a duniya.
Binciken ya nuna cewa wasu gidajen mai sun sayar da fetur a tsakanin ₦1,370 zuwa ₦1,371 a kowace lita, yayin da wasu kuma ke sayarwa a kusan ₦1,361 zuwa ₦1,367 a kowace lita.
Masana sun ce rashin saukar farashin na iya kasancewa saboda tsadar shigo da mai, kudin sufuri da sauran dalilai na cikin gida, duk da raguwar farashin danyen mai a kasuwar duniya.
