Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Ma’aurata Kan Zargin Satar Jarirai

Published

on

images 53

Rundunar ‘Ƴansandan Jihar Ogun State ta kama wata mata tare da mijinta bisa zargin satar jarirai a yankin Mowe, inda jami’ai suka yi nasarar ceto yara uku daga hannunsu.

Mai magana da yawun rundunar, Oluseyi Babaseyi, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Advertisement

Jami’an NDLEA Sun Kama Ƙwayoyi Da Darajarsu Ta Kai Naira Biliyan 480

A cewarsa, waɗanda ake zargin sun haɗa da Oluwarankami Kehinde Ugochukwu da mijinta, Ugochukwu Mathew, waɗanda ake zargi da hannu wajen safarar yara.

Advertisement

Sanarwar ta ce an kama ma’auratan ne bayan wata mata daga yankin Omo Onile ta kai ƙorafi ga ‘yan sanda cewa an sace jaririnta mai wata huɗu a wani asibiti da ke Mowe ranar 17 ga watan Mayu.

images 52

Binciken farko ya nuna cewa matar da ake zargin ta shiga ɗakin mai jego da sunan taimaka mata, kafin daga bisani ta yi awon gaba da jaririn yayin da mahaifiyar ke hutawa bayan karɓar magani.

Advertisement

Bayan samun rahoton, rundunar ta baza jami’an sintiri a tashoshin mota da sauran wurare masu muhimmanci, tare da ƙaddamar da binciken sirri domin gano inda aka kai jaririn.

Daga bisani, jami’an sun kai samame wani maɓoya da ke yankin Kekere Ekun ranar 18 ga watan Mayu, inda suka cafke ma’auratan tare da ceto jaririn da aka sace da kuma wasu yara biyu da aka samu a hannunsu.

Advertisement

‘Yan sanda sun ce bincike ya nuna cewa ɗaya daga cikin yaran da aka ceto an taɓa bayyana ɓatansa tun a shekarar 2024 a irin wannan yanayi.

An miƙa lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar da ke Eleweran a birnin Abeokuta domin ci gaba da bincike.

Advertisement

Kwamishinan ‘Ƴansandan jihar, Bode Ojajuni, ya yaba wa jami’an rundunar bisa saurin ɗaukar mataki, tare da jaddada ƙudirin rundunar wajen yaƙi da safarar yara da garkuwa da mutane a faɗin jihar.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

WIKKI TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending