News
Tirela Ta Hallaka ’Yar Sanda Da Wani Mutum A Gombe
Wata babbar mota ƙirar tirela ta yi ajalin wata jami’ar ’yan sanda da wani mutum a wani mummunan hatsari da ya afku a yankin Sabuwar Mile 3 da ke kan titin Gombe zuwa Yola.
Hatsarin wanda ya faru a ranar Laraba ya kuma jikkata mutane da dama, tare da haddasa asarar dukiyoyi bayan motar ta kutsa cikin babura uku da wasu shaguna da ke gefen hanya.
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Ma’aurata Kan Zargin Satar Jarirai
Rahotanni sun nuna cewa tirelar ƙirar DAF ɗin na ɗauke da buhunan hatsi ne lokacin da direban ya rasa ikon sarrafa motar bayan ya yi yunƙurin shiga hanyar da ba ta dace ba, inda kuma birkin motar ya gaza aiki.
A sakamakon lamarin, wata jami’ar ’yan sanda mai suna Sharifa Gaina ta mutu nan take, yayin da wani mutum da har yanzu ba a tantance sunansa ba shi ma ya rasu a wurin hatsarin.
Mutane da dama ciki har da direban motar sun samu raunuka daban-daban, kuma an garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.
Hatsarin ya kuma lalata babura uku tare da jawo asarar kayayyaki a shagunan da abin ya shafa.
Shaidu sun ce lamarin ya tayar da hankalin jama’a, yayin da jami’an ceto da ’yan sanda suka yi gaggawar isa wurin domin kai ɗauki da kwashe waɗanda suka jikkata.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Gombe, Umar Ahmed Chuso, ya jajanta wa iyalan mamatan tare da kira ga direbobi su riƙa bin dokokin hanya da kula da lafiyar motocinsu domin guje wa aukuwar irin wannan hatsari.
Ya kuma umarci a gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin hatsarin da ɗaukar matakan kariya a gaba.
Shi ma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da addu’ar Allah Ya gafarta musu.
