News
Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Shekaru 15 A Gidan Yari Ba Tare Da Zaɓin Biyan Tara Ba
Wata Babbar Kotun Jihar Legas da ke zamanta a Ikeja ta yanke wa wani mutum mai suna Abdulrahman Lawal Raji hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari bayan samunsa da laifin damfarar Mutum Naira miliyan 26 da sunan samar masa da motar Toyota Hilux.
Mai shari’a Ismail Ijelu ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, bayan kotun ta gamsu cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin da ake tuhumarsa da shi ba tare da wata shakka ba.
An Samu Ƙarin Mutum 274 Da Suka Kamu Da Cutar Kwalara Cikin Sa’o’i 24 A Borno
A cewar Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC), an gurfanar da Raji a gaban kotu ne tun ranar 9 ga Nuwamban 2023 kan tuhume-tuhume biyu da suka shafi damfara.
Hukumar ta ce Raji ya karɓi Naira miliyan 26 daga wani mutum mai suna Olaide Ibidapo, inda ya yi alƙawarin samar masa da motar Toyota Hilux ta ƙirar 2022, amma daga bisani ya kasa kawo motar ko mayar da kuɗin.
Takardun ƙarar sun nuna cewa tsakanin 20 da 21 ga watan Maris na shekarar 2023, wanda ake tuhumar ya karɓi kuɗin ne da nufin damfara, yana mai ikirarin cewa kuɗin farashin motar Hilux ne, alhali ya san hakan ba gaskiya ba ne.
Da aka karanta masa tuhume-tuhumen a gaban kotu, Raji ya musanta aikata laifukan.
A yayin shari’ar, lauyan masu gabatar da ƙara, Ebuka Okongwu, ya gabatar da shaidu huɗu tare da wasu takardu da kotu ta karɓa a matsayin hujjoji. Shi kuma wanda ake tuhuma ya gabatar da shaidu biyu domin kare kansa.
Yayin yanke hukunci, Mai shari’a Ijelu ya ce hujjojin da aka gabatar sun tabbatar da laifin wanda ake tuhuma, don haka ya same shi da laifi.
Kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 kan tuhuma ta farko da kuma shekaru biyar kan ta biyu, ba tare da zaɓin biyan tara ba. Sai dai kotun ta umarci a tafiyar da hukuncin lokaci guda.
Haka kuma, kotun ta umarci Raji da ya mayar wa wanda ya damfara dukkan Naira miliyan 26 da ya karɓa.
Binciken EFCC ya nuna cewa bayan karɓar kuɗin motar, Raji bai samar da motar da aka yi yarjejeniya a kai ba, kuma bai mayar da kuɗin ga mai sayen ba.
