News
Mutane Biyu Sun Mutu, Ɗaya Ya Jikkata A Mummunan Taho Mu Gama Tsakanin Tireloli

Mutane biyu sun rasa rayukansu, yayin da mutum ɗaya ya jikkata bayan wasu tireloli biyu suka yi mummunan taho mu gama a kan titin Sagamu–Ikorodu Expressway da ke yankin Ogijo, a jihar Ogun.
Hukumar Kula da Bin Dokokin Zirga-zirga ta Jihar Ogun (TRACE) ta ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na safiyar Litinin a yankin Kadesh da ke kan hanyar zuwa Ogijo.
Kakakin hukumar, Babatunde Akinbiyi, ya bayyana cewa wani tirela ɗauke da ƙarafa ta yi karo da wata tirela da ke tsaye.
A cewarsa, mutane uku ne ke cikin tirelar da ta yi karo, inda yaron direba da jami’in rakiyar tirelar suka mutu nan take, yayin da direban ya samu raunuka.
Ya ce tirelar mai lambar rajista LND 936 XC ita ce ta haddasa hatsarin, yayin da ɗayan tirelar ya bar wurin kafin jami’an tsaro su samu damar gano cikakkun bayananta.
A wani hatsarin daban da ya faru a wannan rana, mutum biyu sun jikkata bayan wani tirela ɗauke da kayayyakin roba ta kife a yankin Car Park C da ke kan titin Lagos–Ibadan Expressway.
Rahotanni sun nuna cewa tayoyin gaban tirelar guda biyu sun fashe ne yayin da take tafiya, abin da ya sa direban ya rasa ikon tuƙi kafin tirelar ta kife.
Mutane uku ne ke cikin tirelar a lokacin hatsarin, inda biyu suka samu raunuka, yayin da babu wanda ya rasa ransa.
