Connect with us

News

Ilimi Da Addini: Iqra’a Academy Nguru Ta Shirya Bikin Yaye Dalibai Da Masu Haddar Alƙur’ani

Published

on

IMG 20260822 WA0005

‎Makarantar Iqra’a Academy for Science and Islamic Education, da ke Nguru a Jihar Yobe, ta shirya gudanar da bikin yaye dalibai karo na biyu tare da bikin kammala haddar Alƙur’ani, a ranar Lahadi, 23 ga Agusta, 2026.

‎Bikin, wanda zai gudana a Kadawa Daki 9, Nguru, zai ƙunshi karrama ɗaliban da suka kammala matakan karatunsu da kuma waɗanda suka yi nasarar haddace Alƙur’ani.

FBI Ta Ce Ba Za Ta Iya Sakin Wasu Bayanan Binciken Shugaba Tinubu Ba

‎A cewar sanarwar da mahukuntan makarantar suka fitar, za a fara bikin yaye daliban bangaren ilimi da ƙarfe 9:00 na safe zuwa 12:30 na rana.

‎Daliban da za a yaye sun haɗa da waɗanda suka kammala SS3, JSS3, Primary 5 da Nursery 3.

‎Haka kuma, bikin kammala haddar Alƙur’ani zai gudana daga ƙarfe 3:00 na rana zuwa 6:00 na yamma, inda za a karrama ɗaliban da suka kammala haddar Alƙur’ani.

Advertisement

‎Mahukuntan makarantar sun ce bikin zai kasance wata dama ta nuna irin nasarorin da ɗalibai suka samu a fannonin ilimi, haddar Alƙur’ani, tarbiyya da kyawawan ɗabi’u.

‎Sun kuma bayyana cewa makarantar na ƙoƙarin haɗa ilimin kimiyya da na addinin Musulunci domin samar da ɗaliban da za su iya bayar da gudunmawa mai ma’ana ga al’umma.

‎Makarantar ta gayyaci iyaye, malamai, ’yan uwa da sauran al’umma domin halartar bikin da kuma taya ɗaliban da suka kammala karatu da haddar Alƙur’ani murna.

‎Ta ce kasancewar baƙi a wajen bikin zai ƙara masa armashi da daraja, tare da ƙarfafa gwiwar ɗaliban wajen ci gaba da neman ilimi da aiki da abin da suka koya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending