Connect with us

News

EFCC Ta Kwato Sama Da Naira Biliyan 673 Cikin Shekaru Uku

Published

on

EFCC Chairman Ola Olukoyede 1536x864

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta ce ta samu kwato kuɗaɗe da kadarori da darajarsu ta haura dala miliyan 500, wato sama da Naira biliyan 673, cikin shekaru uku da suka gabata.

Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake gabatar da jawabi a taron Cambridge International Symposium on Economic Crime da aka gudanar a ƙasar Birtaniya.

Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano

Olukoyede ya ce nasarar ta samu ne sakamakon amfani da dokokin ƙasar da ke bai wa EFCC damar neman kwace kadarorin da ake zargin an samo su daga aikata laifukan tattalin arziki, ba tare da jiran kammala shari’ar laifi ba.

Ya bayyana cewa daga cikin kadarorin da hukumar ta kwato akwai wani jirgin sama da aka danganta da wani mutum da ake zargin ya karɓi cin hancin dala miliyan 30. Ya ce kotu ta amince da kwace jirgin, wanda daga bisani aka shigar da shi cikin tawagar jiragen gwamnatin Najeriya.

Shugaban EFCC ya kuma bayyana kwato wani katafaren rukunin gidaje mai ɗauke da gidaje 753 da ke Abuja, wanda aka danganta da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Advertisement

Baya ga haka, Olukoyede ya ce hukumar ta samu umarnin kwace kadarori 57 da ake dangantawa da tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami. A halin yanzu, EFCC ta ce tana neman a mayar da kwacen ya zama na dindindin.

Olukoyede ya danganta nasarorin hukumar da ƙwarewar jami’anta da kuma horon da suke samu daga manyan cibiyoyin yaƙi da cin hanci da rashawa a duniya, yana mai cewa hakan na ƙara musu ƙwarewa wajen bincike da kwato dukiyar da ake zargin an samo ta ta haramtacciyar hanya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending