Labarai
Ƙungiyar Arewa Women Health ta gudanar da taron Makon ’Ya Mace a Kano

Ƙungiyar Arewa Women Health ta gudanar da bikin Makon ’Ya Mace (Girl Child Week) a Kano, da nufin wayar da kan al’umma kan muhimmancin kare haƙƙin ’ya mace, ba ta ilimi da kuma ƙarfafa mata gwiwa domin ta cimma burinta.
An gudanar da taron ne a ɗakin taro na British Council da ke Kofar Nassarawa, Kano, ƙarƙashin taken “Protect Her Future, Educate Her, Empower Her”, wanda ke nufin kare makomar ’ya mace, ilimantar da ita da kuma ƙarfafa mata gwiwa.
Majalisar dattawa ta miƙa wa Tinubu ƙudirin samar da ƴansandan jihohi
Taron ya ƙunshi shirye-shirye daban-daban da suka haɗa da wayar da kai, baje kolin kayayyaki da ayyukan kula da mata, da kuma gasa tsakanin ’yan mata domin nuna ƙwarewarsu.
Da take magana kan tarihin ƙungiyar, shugabar Arewa Women Health, Amina, ta bayyana cewa an kafa ƙungiyar ne a shekarar 2020, kuma wannan ne karon farko da ta shirya irin wannan taro na Makon ’Ya Mace.
Ta ce an kuma gudanar da gasa daban-daban tare da bayar da kyaututtuka ga waɗanda suka yi nasara, ciki har da zaɓen Sarauniyar ’Ya Mace (Queen of the Girl Child), domin ƙarfafa wa ’yan mata gwiwa da kuma ba su damar nuna basirarsu.
Taron ya samu halartar wakilin Dan Malikin Kano, Auwal Madu Yakasai, da mataimakiyar shugabar ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa, Ambassador Hannatu.
A jawabansu, sun jaddada muhimmancin bai wa ’ya mata ilimi, kariya da damar taka rawa a ci gaban al’umma, suna mai cewa bai wa ’ya mace damar samun ilimi da bunƙasa ƙwarewarta na da muhimmanci wajen gina al’umma mai nagarta.
-
Kasuwanci1 day ago
PAN Ta Bukaci Gwamnatoci Su Bai Wa Noma Da Kiwo Muhimmanci Kamar Tsaro
-
Labarai5 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai4 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
