Connect with us

Labarai

KANO: Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mutane 3 Kan Zargin Fashi Da Garkuwa A Rogo

Published

on

IMG 20261123 235256 690
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama mutane uku bisa zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma cin zarafin wata mata a ƙaramar hukumar Rogo.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 23 ga Nuwamba, 2026.

Dakarun Sojin Sama Sun Hallaka ‘Yanta’adda 37 A Borno

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 3 ga Nuwamba, da misalin ƙarfe 2:00 na rana, a ƙauyen Aleko da ke Rogo, inda waɗanda ake zargin suka kutsa cikin gidan wani mazaunin ƙauyen ɗauke da makamai.

A cewarsa, maharan sun ci zarafin wata mata, sannan suka sace babur ƙirar Boxer mai darajar Naira miliyan 1.15 da buhunan barkono busassu 25 da aka ƙiyasta kuɗinsu ya kai Naira 850,000.

Ya ce mai gidan ya gane ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, Nafi’u Lawal, wanda aka fi sani da Gamji, lamarin da ya taimaka wajen cafke su.

Advertisement

Waɗanda aka kama sun haɗa da Nafi’u Lawal, mai shekaru 21; Auwalu Shafi’u, mai shekaru 26, wanda aka fi sani da Bakin Tuwo, da Yunusa Sale, mai shekaru 26, wanda aka fi sani da Bammi.

Kiyawa ya ce yayin bincike, waɗanda ake zargin sun amsa laifin, tare da bayyana hannu a wasu hare-haren garkuwa da mutane guda biyu, ciki har da na Ibrahim Iro, wanda aka fi sani da Dangi, da Shadari, wanda aka fi sani da Ardo.

Ya ce waɗanda aka yi garkuwa da su an sake su ne bayan an biya kuɗin fansa na Naira 900,000 da kuma Naira miliyan ɗaya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending