Labarai
Wasu Ƴan Bindiga Sun Hallaka Mutane 16 A Plateau

Aƙalla mutum 16 ciki har da mata da matasa da ƙananan yara sun mutu yayin da wasu huɗu su ka jikkata bayan wasu ƴan bindiga sun kai hari al’ummar Tafi Gana da ke kusa da Jebbu Miango, a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Plateau.
Ƙungiyar raya al’ummar Irigwe (IDA) ce ta bayyana hakan, inda ta ce maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren Laraba, 25 ga Nuwamba, 2026, ɗauke da bindigogi da sauran makamai, su ka riƙa harbe-harbe kan mai uwa da wabi.
Hukumar Shari’a Ta Kano Ta Nemi Haɗin Gwiwar ’Yan Jarida Wajen Yaƙi Da Cin Mutunci A Soshiyal Midiya
Ta ce zuwa safiyar Alhamis, an tabbatar da mutuwar mutum 16, yayin da wasu huɗu su ka samu raunuka.
Ƙungiyar ta ce an kai rahoton lamarin ga jami’an tsaro, waɗanda su ka isa wurin da harin ya faru. Ta kuma yi Allah-wadai da kisan, tare da kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, kada su ɗauki doka a hannunsu, su bar jami’an tsaro su gudanar da bincike da tabbatar da adalci.
-
Labarai4 days ago
Dakarun Soji Sun Kuɓutar Da Yara 18 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna
-
Labarai15 hours ago
BAYAN WATA SHIDA: Shugaba Tinubu Ya Yi Alƙawarin Kuɓutar da Ɗaliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Borno
-
Wassanni3 days ago
Najeriya Ba Ta Kai Matsayin Da Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kofin Duniya Ba —Shugaban FIFA
