Connect with us

News

Yan fashi sun tare motar banki tare da kwashe kudi

Published

on

motar banki

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

‘Yan sanda a jihar Abiya da ke kudu maso gabashin Najeriya sun tabbatar da harin ‘yan fashi kan motar dakon kudi ta banki dauke da makudan kudade.

 

Advertisement

Jaridar Vanguard a Najeriya ta ruwaito cewa motar na kan hanyarta ne daga birnin Aba zuwa Umuahia.

Buhari Yaba Da Umarnin Fito Da Jirage Don Fara Sufuri A Kamfanin Nigerian Air

Advertisement

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar SP Geoffrey Ogbonna, ya ce ‘yan fashin sun yi wa motar kwantan bauna ne a kan babbar hanyar Enugu zuwa Fatakwal, abin da ya tilasta wa direban motar kauce wa hanya

 

Advertisement

SP Ogbonna ya ci gaba da cewa wani jami’in banki da ke yi wa motar kudin rakiya, tare da dan fashi daya sun rasa ransu a lokacin aukuwar lamarin, yayin da ‘yan sanda uku suka jikkata.

 

Advertisement

Rahotonni sun ce a lokacin harin ‘yan fashin sun yi awon gaba da kudin da ba a iya tantance adadinsu ba

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending