Connect with us

News

Kwamitin Sulhu Na Majalisar Dinkin Duniya Zai Yi Zaman Gaggawa Akan Yakin Falasdinawa Da Isra’ila

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Har yanzu babu wata alamar tsayawa a yakin da ake gwabzawa a zirin Gaza sakamakon cigaba tashin bama-bamai da kuma harba makaman roka da ake yi.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani taron gaggawa a yau kan matsalar gudanar da aiyukan jin kai a yankin, bayan da Isra’ila ta fadada kai hari Falasdinu a karshen mako.

Advertisement

Ana ci gaba da aikin gano mutane 104 da jirgin ruwa ya kife da su a jihar Taraba

A yayin taron wanda Hadaddiyar Daular Larabawa ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar zai tattauna kan matsalolin gudanar da aiyukan jin kai a falasdinu.

Ya zuwa yanzu dai kwamitin sulhun ya gaza daukar wani mataki a yunkurin da aka yi na tsagaita wuta har sau hudu, tun bayan da kasashen Rasha da Amurika suka hau kujerar na’ki.

Advertisement

A wani labarin kuma Ana ci gaba da aikin gano mutane 104 da jirgin ruwa ya kife da su a jihar Taraba

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending