News
An sace takardun Shigar da kara a Kotun Sauraren Korafe-Korafen Zaben Jihar Kogi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
‘Yan Bindiga sun sace takardun Shigar da kara na Jam’iyyun AA da PRP da SDP da APP da suke kalubalantar Nasarar APC a Zaben Gwamnan Jihar Kogi.
Sakataren Kotun David Mike shiya shaida Hakan ga Rundunar ‘Yan Sanda, inda yace mutane da suka dauke da bindigu sun tareshi akan hanya tare da kwace dukkanin takardun Shari’a da Jam’iyyu 4 suka shigar suna kalubalantar Nasarar Usman Ododo Sabon zababben Gwamnan Jihar Kogi Mai Jiran Gado Karkashin Jam’iyyar APC.
Kungiyar Hezbollah da Isra’ila sun yi musayar wuta yayin da ake fuskantar tashin hankali a kan iyaka
DAILY POST ta rahoto cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Usman Ododo a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Babban abokin hamayyarsa, Murtala Ajaka na SDP, ya shigar da kara a kotun jihar yana neman soke nasarar APC.
