Connect with us

News

Ƴan Majalisar Wakilai Sun Nemi Da A Dakatar Da Mele Kyari

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ƴan majalisar wakilai a ƙarkashin ƙungiyar The Economy Rescue Group Su 15 , sun nemi da a dakatar da shugaban rukunin kamfanin mai na Najeriya Mele Kyari.

Advertisement

Ƙungiyar ta yi ikirarin cewa rashin tafiyar da tsare tsare karkashin jagorancin Kyari a NNPC ne ke jawo ƙalubalen da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke fuskanta.

Kano Pillars Ta Sallami Sabon Mai Horos Da Kungiyar Wanda Ta Dauka Kasa Da Wata Guda

Leadership ta ruwaito cewa A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Abuja kuma shugabanta ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Oredo, Esosa Iyawe, shi ne ya sanyawa hannu kuma aka saki a ranar Talata,inda ƙungiyar ta dage cewa a dakatar da Kyari har sai an samu sakamakon kwamitin hadin gwiwa na majalisar wakilai game da binciken kwakwaf da ake yi na Petroleum Downstream and Midstream game da halin da kamfanin mai na kasa ke ciki.

Advertisement

Haka kuma ƴan majalisar na zargin shugaban kamfanin na NNPC da sauran ma’aikatan gudanarwar da yi wa Tinubu’s Renewed Hope Agenda zagon kasa.

Sun kuma nemi da dole ne a cire Kyari da tawagarsa har sai an kammala binciken kwakwaf da kwamitin hadin gwiwa na Majalisar Wakilai na Downstream and Midstream Ke gudanarwa don gujewa duk wani abu na zagon kasa.

Advertisement

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Mu ‘yan majalisa mai ɗauke da mutane 15 mun lura cewa ko shakka babu matsalolin da ake fuskanta a bangaren man fetur da iskar gas a gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya samo asali ne sakamakon gazawa da rashin gudanar da ayyukan hukumar ta NNPC a karkashin jagorancin Kyari. Don haka, don warware waɗannan matsaloli dole ne su yi murabus.

“Tunda sun kasa sauka da kansu, to bai kamata shugaban kasa ya yi kasa a gwiwa ba wajen dakatar da su har sai an gama gudanar da binciken da majalisar wakilai ke gudanarwa kan harkokin man fetur.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending